Kwankwaso ya shiga NDC
Kwankwaso Ya Tabbatar da Shiga NDC.
Yayi Kira da Goyon Bayan Jama’a Kan Sabuwar Gwagwarmaya Ta DimokuraɗiyyaA cewar Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jiya an ɗauki wani muhimmin mataki mai ƙarfi ta hanyar shiga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a hukumance.
Ya bayyana hakan ne a gidan Sanata Seriake Dickson da ke Abuja, inda ya ce wannan mataki ya samo asali ne daga ƙuduri mai zurfi na kare ƙimar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Kwankwaso ya ce sabon matakin zai taimaka wajen samar wa al’umma ingantaccen dandali da zai ba su damar bunƙasa tare da cimma cikakkiyar damar su a fannoni daban-daban.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa masu jajircewa, tare da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa, da su shiga jam’iyyar NDC domin haɗa kai wajen gina sabon tsarin shugabanci mai nagarta da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya ta gaskiya.

Hoto: Facebook/ Rabiu Musa Kwankwaso