NDC Ta Fitar Da Sabon Tsari a Kano
Jam’iyyar NDC ta kammala fitar da tsarin shugabanci a Jihar KanoJam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta sanar da kammala tsara sabon tsarin shugabancinta a Jihar Kano, a wani mataki da take cewa zai taimaka wajen ƙarfafa tafiyar da harkokin jam’iyyar da tabbatar da ingantaccen shugabanci a matakin jiha.Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke ƙoƙarin daidaita tsarin cikin gida da kuma magance sabanin da ya taso bayan shigowar sabbin manyan ‘yan siyasa cikin jam’iyyar a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma matsaya kan rabon mukamai da kuma yadda za a tsara ayyukan shugabanci, domin tabbatar da cewa dukkan ɓangarori sun samu wakilci cikin tsarin jam’iyyar.Haka kuma, shugabannin jam’iyyar sun jaddada muhimmancin haɗin kai da bin doka, tare da kira ga mambobi da su ci gaba da aiki cikin lumana domin ƙarfafa jam’iyyar a Kano da kuma faɗin ƙasa baki ɗaya.
Wannan sabon tsarin na daga cikin matakan da NDC ke ɗauka domin shirin tunkarar zaɓe mai zuwa tare da ƙarfafa ginshiƙin jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa.
