Gwamnatin Tarayya Ta Takaita Amfani da “Dr” na Girmamawa a HukumanceMinistan Ilimi na ƙasa

Gwamnatin Tarayya Ta Takaita Amfani da “Dr” na Girmamawa a HukumanceMinistan Ilimi na ƙasa, Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da wata sabuwar matsaya da za ta takaita amfani da taken “Dr” ga masu digirin girmamawa (honorary doctorate) a harkokin hukuma.

Ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba, inda ya ce an cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (FEC) da aka gudanar ranar 30 ga watan Afrilu.A cewar ministan, matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na gyara tsarin ilimi da kuma kare martabar digirin digirgir (PhD), domin guje wa ruɗani tsakanin masu digirin karatu na gaskiya da kuma waɗanda aka karrama da digirin girmamawa kawai.

Sabuwar dokar na nufin cewa duk wanda bai mallaki digirin digirgir ta hanyar karatu ba, ba zai riƙa amfani da taken “Dr” a hukumance ba, duk da cewa ana iya ci gaba da girmama shi da irin wannan karramawa a al’umma.Ana sa ran wannan mataki zai ƙara inganta gaskiya da darajar ilimi a Najeriya, tare da tabbatar da cewa ana amfani da mukamai daidai da cancanta.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *