APC Ta Kaɓi Fom Ɗin Takarar Shugaba Tunubu

APC Ta Karɓi Fom ɗin Tinubu, Ta Jaddada Ci Gaba da Hadin Kai a ƘasaA yau da safe, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya jagoranci Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar wajen karɓar fom ɗin nuna sha’awa da na takarar shugaban ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR), a wani gagarumin taro da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa (ICC), Abuja.
Taron ya samu halartar gwamnoni, ’yan Majalisar Tarayya, shugabannin jam’iyya, dattawa, da sauran manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ya nuna ƙarfin haɗin kai da goyon bayan da jam’iyyar ke da shi a faɗin Najeriya.
A cikin jawabin, an bayyana cewa yawan jama’ar da suka halarci taron da kuma nuna goyon baya mai ƙarfi ga Shugaba Tinubu, ya ƙara tabbatar da amincewar ’yan jam’iyya da ’yan Najeriya ga tsarin Renewed Hope Agenda da manufar jagorancinsa.
An bayyana taron a matsayin ba kawai na karɓar fom ba, illa wata muhimmiyar alama ta haɗin kai, ci gaba da kuma ƙudurin ƙara ƙarfafa nasarorin da ake samu a ƙarƙashin wannan gwamnati.Jam’iyyar APC ta jaddada aniyarta ta ci gaba da ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida, inganta haɗin kan ƙasa, da kuma tallafa wa manufofi da shirye-shiryen da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
A ƙarshe, jam’iyyar ta bayyana cewa tana ci gaba da tafiya da sabon ƙuduri da jajircewa domin gina Najeriya mai ƙwari, haɗaɗɗiya da ƙarfin tattalin arziki.