Kafin Farmakin Anyi Korafi Da A Dauki Mataki Kan Kalaman Malam
An kashe matashin da ya farmaki Malam Musa Lukawa a masallaciWani rikici ya barke a birnin Sokoto a ranar Juma’a, bayan wani matashi ya kai wa malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukawa, hari da wuƙa jim kaɗan bayan ya jagoranci Sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera.Rahotanni sun ce matashin, wanda yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, yana zaune ne a ɗaya daga cikin sahun gaba kafin ya kai wa malamin farmaki nan take bayan an kammala sallar. An ce ya daba wa Malam Lukawa wuƙa sau biyu a wuya, lamarin da ya jikkata malamin.Bayan harin, wasu daga cikin masu ibadar da ke masallacin sun yi nasarar cafke matashin. Sai dai rahotanni sun ce wasu fusatattun matasa sun lakada masa duka har ya mutu a wurin.Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da wasu ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci suka gabatar da ƙorafi ga gwamnatin Jihar Sakkwato da kuma Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi kan wasu kalamai da ake dangantawa da Malam Musa Lukawa.Ƙungiyoyin malaman da suka haɗa da wasu daga ƙungiyar Sufaye ta Tijjaniya da zuri’ar Sheikh Usmanu Danfodiyo, da sauran malamai, sun ce suna damuwa kan wasu kalaman da suke zargin suna taɓa martaba da matsayin Annabi Muhammad ﷺ.Malaman sun buƙaci hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa, suna gargadin cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da fitina da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar Musulmi.Sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa farmakin matashin yana da alaƙa kai tsaye da ƙorafin malamai ba. Hukumomin da abin ya shafa ne za su iya tabbatar da dalilin harin bayan gudanar da cikakken bincike.Lamarin ya ƙara jaddada buƙatar a bar doka ta bi hanyarta wajen magance irin waɗannan matsaloli, maimakon ɗaukar doka a hannu.
