Uba Sani ya ziyarci iyalin Malam Ahmed Zakka da aka ceto, ya ce Gwamnati za ta ba su gida
Uba Sani ya ziyarci iyalin Malam Ahmed Zakka da aka ceto, ya ce Gwamnatin Kaduna za ta ba su gida.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ziyarci Malam Ahmed Abubakar Zakka, matarsa Nafisah da ɗiyarsu Fatima a gidan kariya na Gwamnatin Jihar Kaduna, inda suke ci gaba da samun kulawar likita bayan sun bar asibiti, sun kuma sami ‘yanci.
Gwamnan ya ce ya ji daɗin ci gaban da iyalin ke samu, kuma yana da bege za su warke sarai.
Ya bayyana abin da suka shiga a matsayin tunatarwa mai raɗaɗi kan asarar da rashin tsaro ke jawowa, da kuma nauyin da ke kan gwamnati na kare rayuka da dawo da zaman lafiya a kowace al’umma.
Uba Sani ya tabbatar wa iyalin cewa tallafin gwamnati ba zai tsaya a wannan ziyara ba.
A cewarsa, Gwamnatin Kaduna za ta ba su gida da biya dukkan kuɗin magani, sannan ta samar musu da kulawar ƙwaƙwalwa da zamantakewa mai ɗorewa, domin su warke, su sake gina rayuwarsu, su kuma dawo da kwanciyar hankali.
Ya ce ‘yantar da iyalin ya ƙara ƙarfafa ƙudurin gwamnatin na yaƙi da ‘yan bindiga da sauran laifuka, ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, ƙarfafa tsare-tsaren tsaro da kusanci da al’ummomi.
Ya ƙara da cewa kowane mazaunin jihar na da haƙƙin rayuwa ba tare da tsoro ba.Gwamnan ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kulawarsa ta kai-tsaye kan lafiyar iyalin.
Ya kuma yaba wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da hukumomin tsaron ƙasar kan gagarumar gudunmawarsu wajen dawo da iyalin lafiya.A nasa ɓangaren, Malam Ahmed ya gode wa Gwamnatin Tarayya, ta Jihar Kaduna da hukumomin tsaro kan ƙoƙarinsu da tausayinsu.
Gwamnan ya ce yadda yake godiya da kulawar da yake samu da kuma kwarin gwiwarsa na warkewa abin ƙarfafa gwiwa ne, kuma lafiyarsu da warkewarsu za su ci gaba da zama abin fifiko ga gwamnatinsa a watanni masu zuwa.
Sanarwar ta fito daga Gwamna Uba Sani ranar 20 ga Oktoba, 2026.

