File 00000000c36081f5ad4375fa73211610

CBN YA RAGE KUDIN RUWA ZUWA KASO 23

Rage kuɗin ruwan CBN zai shafi ’yan Najeriya.

’yan kasuwa da masu zuba jari ta hanyoyi daban-dabanRage ƙimar manufofin kuɗi (Monetary Policy Rate – MPR) da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zai iya yin tasiri ta hanyoyi daban-daban ga ’yan Najeriya, ’yan kasuwa, masu zuba jari da gwamnati.A ranar Talata, CBN ya rage MPR — wato babban ma’aunin da ake amfani da shi wajen tsara farashin riba a tsarin banki — da maki 350 (350 basis points), daga kashi 26.5 zuwa kashi 23.

Wannan shi ne rage MPR na farko da CBN ya yi a shekarar, kuma ya kai ƙimar ribar zuwa mafi ƙarancin mataki tun Fabrairu 2024, lokacin da take kashi 22.75.A takaice, rage MPR na iya sanya ribar rance ta ragu, wanda zai iya taimaka wa wasu ’yan kasuwa da masu neman rance.

Haka kuma, masu ajiya da masu zuba jari na iya fuskantar sauye-sauye a ribar da suke samu daga wasu kayayyakin kuɗi.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *