Atiku Ya Gana Da Jagoran TMG
Atiku Abubakar: Na karɓi tawagar masu fafutukar “Tinubu Must Go”.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ya ce ya karɓi bakuncin Barrister Abba Hikima, ɗaya daga cikin manyan masu shirya fafutukar “Tinubu Must Go” (#TMG) ta ƙasa baki ɗaya.
Atiku ya ce ziyarar ta biyo bayan kammala wani zaɓen jin ra’ayin jama’a da ƙungiyar ta gudanar a faɗin ƙasar, wanda ya samu halartar mutane 109,799.
Ya ce abin da ya fi ƙarfafa masa gwiwa shi ne yadda aka samu dimbin shiga da ra’ayin jama’a a wannan aikin.
A cewarsa, kamar yadda sakamakon zaɓen ya nuna, takararsa ta samu kashi 73.6 cikin 100 na ƙuri’un, yayin da aka bayyana ADC a matsayin dandalin siyasa da aka fi so.
Atiku ya ce abin da ya fi muhimmanci ba wai sakamakon zaɓen kaɗai ba ne, illa abin da yake wakilta na ƙara samun buƙatar sauyi a tsakanin wasu ’yan Najeriya da kuma yunƙurin neman wata sabuwar alkibla ga ƙasar.
Ya bayyana cewa yana goyon bayan wannan fafutuka, tare da gayyatar ’yan Najeriya masu ra’ayi irin wannan da su shiga ƙungiyar.
Atiku ya kuma ce yana fatan tattaunawa da sauran shugabannin ƙasa na ƙungiyar Tinubu Must Go, domin yin aiki tare kan manufar sake gina Najeriya mai haɗin kai, wadata da dimokuraɗiyya.

