157757

Lauya Ya Kai Karar Surukansa Kotu

Lauya ya kai surukansa kotu kan zargin hana shi auren ’yarsu.

Wani lauya a Kano ya maka surukansa a kotu, bisa zargin cewa sun kawo cikas ga shirin aurensa da ’yarsu, duk da cewa a cewarsa sun riga sun cimma matsaya kan auren.

Lauyan ya ce ya kashe kusan Naira miliyan 6 wajen shirye-shiryen auren, kuma ya zargi mahaifiyar yarinyar da fara kawo matsaloli bayan an samu fahimtar juna tsakaninsa da ’yarta.

Ya bayyana cewa har an gudanar da gwajin jini na halitta (genotype) tsakanin su, kuma babu wata matsala da aka gano.

A cewar rahoton Daily Nigeria Hausa, lauyan ya kuma zargi wani malamin Islamiyya da yin tasiri kan yarinyar, lamarin da ya ce ya kara kawo tsaiko ga shirin auren.

Lauyan ya ce ya kai batun kotu ne domin neman shiga tsakani da warware matsalar. Ya kuma bayyana cewa idan aka samu sulhu tsakanin bangarorin, zai amince da shi.An ce yarinyar tana zaune ne a unguwa ta Fagge, bayan Audu Karfe, Kano.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *