Peter Obi Ya Koma Da Baya Kan Batun Dawo Da Tallafin Fetur
Obi ya sauya matsayinsa, ya ce zai dawo da tallafin man fetur bayan yaki da cin hanci..
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), ya ce idan aka kafa gwamnatinsa, zai dawo da tallafin man fetur bayan an magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa da aka shirya domin tikitin takarar Obi/Kwankwaso a Sokoto.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya taba sake jaddada a watan Agusta cewa yana goyon bayan janye tallafin man fetur.Hakan ya nuna sauyin matsayi daga bayanan da ya bayyana a baya, inda ya kasance cikin masu goyon bayan cire tallafin.

