Pantsami Ya Sake Lashe Tikitin Gwamna Na PDP
Pantami ya sake lashe tikitin PDP na takarar gwamnan Gombe.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sake lashe tikitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.
Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na PDP da aka gudanar a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, inda ya samu kuri’u 817.
Khamisu Ahmed Mailantarki ya zo na biyu da kuri’u 153, yayin da Aliyu Usman Garry ya samu kuri’u 50. An gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 11 na jihar.
Wannan shi ne karo na biyu da Pantami ya samu tikitin PDP bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na farko da aka gudanar a watan Mayu.
Sai dai Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke nasarar farko a ranar 24 ga Satumba, 2026, bayan Usman Garry da Khamisu Mailantarki sun kalubalanci tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta ce a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa tsarin mulkin PDP, ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin zaɓe.Bayan hukuncin kotun, PDP ta sanya ranar 29 ga Satumba, 2026 domin gudanar da sabon zaɓen, tare da tantance Pantami, Mailantarki da Garry a matsayin ‘yan takarar da za su fafata.
A sabon zaɓen da aka gudanar yau, Pantami ya samu kuri’u 817 daga cikin kuri’un da aka bayyana, inda ya doke abokan hamayyarsa biyu, Mailantarki da Garry.
Pantami dai ya koma PDP ne bayan ya janye daga neman tikitin APC na takarar gwamnan Gombe, bayan jam’iyyar ta karkata ga Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta. Daga bisani ya koma PDP, inda ya samu tikitin jam’iyyar a karon farko ta hanyar amincewar wakilan jam’iyyar.
Da wannan sabuwar nasara, Pantami ya sake zama ɗan takarar PDP na neman kujerar gwamnan Gombe a zaɓen 2027, duk da cewa batun tsarin da aka bi wajen zaɓen farko ya kai ga kotu tare da haifar da sabon zaɓen fidda gwani.

