158029

Bayyana Pantami Ya Sake Samun Tikiti, Rikici Ya Sake Kunno Kai A PDP

Gombe PDP: An sake zaɓen fidda gwani, Pantami ya sake samun tikiti..

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna domin maye gurbin zaɓen farko da wata kotu ta soke.

A sabon zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Satumba 2026, Prof. Isa Ali Pantami ya sake fitowa a matsayin wanda ya samu nasara.

Pantami ya samu ƙuri’u 2,054, yayin da Khamisu Ahmed Mailantarki ya samu 389, sannan Usman Aliyu Garry ya samu 112.

An gudanar da zaɓen a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, sannan kwamitin zaɓen ya tattara tare da bayyana sakamakon a hedikwatar PDP ta jihar da ke Gombe. Sai dai Mailantarki ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya ce zai ci gaba da ƙalubalantar batun a kotu.Kotun ta soke zaɓen farko.

Wannan sabon zaɓen ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe na ranar 24 ga Satumba 2026, wadda ta soke tsarin zaɓen fidda gwani na farko da aka gudanar a watan Mayu, wanda ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP.

Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta umurci PDP da ta gudanar da sabon zaɓen cikin kwanaki 30, bayan kotun ta gano cewa tsarin zaɓen farko bai bi wasu ƙa’idojin jam’iyyar da tanade-tanaden dokar zaɓe ba.

Shari’ar ta samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafen Khamisu Mailantarki da Usman Aliyu Garry, waɗanda suka ƙalubalanci yadda Pantami ya samu tikitin PDP a zaɓen farko.Sai dai kotun ba ta amince da buƙatar a cire Pantami daga zama ɗan PDP ko kuma a hana shi shiga sabon zaɓen ba. Mailantarki ya sake kalubalantar PantamiBayan sabon zaɓen, Mailantarki ya bayyana cewa ba zai amince da abin da ya faru ba.

Ya yi ikirarin cewa tun farko sunansa da na Usman Garry ne aka miƙa wa INEC, ba tare da sunan Pantami ba.A cewarsa, tun da kotu ta soke zaɓen farko tare da bayar da umarnin sake gudanar da shi, har yanzu akwai batun cancantar Pantami da yake ganin ya kamata a sake dubawa.

Mailantarki ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya samu halastattun ƙuri’u masu rinjaye, amma aka bayyana Pantami a matsayin wanda ya yi nasara.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da DCL Hausa, inda ya ce ba za su amince da sakamakon ba kuma za su koma kotu.

A gefe guda, rahotannin kotun sun nuna cewa ƙalubalen da Mailantarki da Garry suka shigar tun farko bai kai ga hukuncin cire Pantami daga PDP ko hana shi shiga sabon zaɓen ba.

Batun rajistar mambobin PDPƘungiyar lauyoyin masu ƙalubalantar Pantami ta kuma yi zargin cewa Pantami bai cikin jerin sunayen mambobin PDP da aka miƙa wa INEC cikin wa’adin da doka ta tanada kafin zaɓen fidda gwani.

Lauyoyin sun ce wannan batu na da alaƙa da Sashe na 77 na Electoral Act 2026, wanda ya shafi rajistar mambobin jam’iyya da amfani da ita wajen gudanar da zaɓen fidda gwani. Sun kuma sanar da cewa an shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da neman dakatar da sabon zaɓen da Pantami zai shiga.

Sai dai PDP ta share Pantami, Mailantarki da Garry domin shiga sabon zaɓen da aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga Satumba. A halin yanzu, PDP ta ayyana Pantami a matsayin wanda ya lashe sabon zaɓen, amma Mailantarki ya nuna cewa zai ci gaba da bin hanyar shari’a domin ƙalubalantar sakamakon da kuma batun cancantar Pantami.

Wannan na nufin rikicin shari’a kan tikitin PDP na Gombe zai iya ci gaba bayan kammala sabon zaɓen.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *