APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku, ta ce ƙulle-ƙullen siyasa ne
APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku, ta ce ƙulle-ƙullen siyasa ne.
Jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da zargin cewa akwai wani shiri na kashe tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, yayin da yake amsa zargin da wani ɗan ADC, Timi Frank, ya yi.
Alake ya ce Shugaba Bola Tinubu, Fadar Shugaban Ƙasa da jam’iyyar APC ba su da hannu a kowane shiri na cutar da Atiku ko wani jigo na jam’iyyun adawa.
Sanarwar ta kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaron da ke kare Atiku. Ta ce yana ci gaba da samun cikakkiyar kariya daga ‘yan sanda da hukumar DSS.
BBC Hausa ta ruwaito cewa Dele Alake ya bayyana zargin kisan a matsayin ƙulle-ƙullen siyasa irin na jam’iyyun adawa, da nufin zafafa siyasar ƙasar da jawo hankalin ƙasashen duniya ta kafafen sada zumunta.
Ya ƙara da cewa a kwanan nan Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ƙarfafa tsaron da ake bai wa duk ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakan shugaban ƙasa, da gwamnoni da mataimakansu, gabanin babban zaɓen 2027.
Kwamitin ya jaddada cewa duk wata barazana ga rayuwar ɗan ƙasa abu ne mai haɗari da ke buƙatar mataki ba tare da la’akari da siyasa ba. Ya kuma yi kira ga Timi Frank da ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaggawa.

