Shari’ar Emefiele: Masu ƙara sun ce wasiƙun da aka fitar $6.23m na jabu ne
EFCC ta nemi kotu ta yi watsi da roƙon Emefiele na cewa babu shari’a a kansa
Hukumar Yaƙi da Rashawa da Laifukan Kuɗi (EFCC) ta roƙi Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja, da ta yi watsi da roƙon “babu shari’a” (no-case submission) da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya shigar.
NTA ta rawaito cewa Hukumar ta dage cewa shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatar sun tabbatar da shari’a ta farko (prima facie case) da ke buƙatar Emefiele ya shiga kare kansa.
Emefiele na fuskantar ƙarar da aka gyara ta tuhume-tuhume 20, wadda ta ƙunshi zargin keta amana, jabu, amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba, maƙarƙashiya da karɓar kuɗi ta hanyar ƙarya.
Ƙarar ta ƙunshi kuma zargin fitar da dala miliyan 6.23 da bai wa wasu fa’ida ta cin hanci wajen bayar da kwangilolin CBN.Lauyan masu gabatar da ƙara, Daraktan Gabatar da Ƙara na Tarayya, Rotimi Oyedepo (SAN), ya bayyana cewa manufar roƙon “babu shari’a” ita ce tantance ko masu ƙara sun kafa shari’a ta farko, ba tantance laifin wanda ake tuhuma ko amincin shaidu a wannan mataki ba.
Dangane da zargin fitar da dala miliyan 6.23, masu ƙara sun ce an fitar da kuɗin daga CBN tsakanin watan Fabrairu da Yuni, kafin a cire Emefiele daga mukaminsa, bisa wasiƙun da aka ce na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.
Oyedepo ya ce shaidu, ciki har da Mustapha da wani masanin binciken jabu (forensic analyst), sun nuna cewa wasiƙun da aka yi amfani da su wajen sakin kuɗin jabu ne.
A nasa ɓangaren, lauyan Emefiele, Mathew Burkaa (SAN), ya roƙi kotu ta sallami wanda yake karewa, yana mai cewa masu ƙara sun gaza kafa muhimman abubuwan da shari’ar ke buƙata.Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ce za a sanar da ɓangarorin ranar da za a yanke hukunci kan roƙon.

