EFCC ta gurfanar da ɗan Saliyo kan zargin damfarar $190,324 a Legas
EFCC ta gurfanar da ɗan Saliyo kan zargin damfarar $190,324 a Legas
Hukumar Yaƙi da Rashawa da Laifukan Kuɗi (EFCC), Shiyyar Legas ta 2 da ke Ikoyi, ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Saliyo, Favour Foday Kamara, kan zargin damfarar dala $190,324, ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, a gaban Mai Shari’a O. A. Okunuga na Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja.
Mai ƙara, Henrietta Vandi, ‘yar Saliyo mai shekara 70 da ke zaune a Amurka, ta yi zargin cewa ta haɗu da wanda ake tuhuma ne a lokacin ziyararta zuwa Cocin Synagogue Church of All Nations tsakanin 2019 da 2020.
Ta ce daga baya ya ƙarfafa mata gwiwa ta zuba jari a Najeriya yayin haduwarsu.
Bincike ya nuna cewa Vandi ta aika kuɗi ta hanyar Ria, Western Union, MoneyGram da tura kuɗi hannu da hannu zuwa asusun Access Bank na wanda ake tuhuma, domin sayen gida da gyara shi a Titin Gbenga Ogunleye/Atobatele, Cele Bus Stop, Araromi, Alimosho, Legas.
Binciken ya kuma nuna cewa an saya gidan ne da sunan wanda ake tuhuma, shi ne ke zaune a ciki kuma yana karɓar kuɗin haya daga masu haya.Bayan kammala bincike, an gurfanar da shi a kan tuhuma biyu na zargin sata da karkatar da kuɗi ta hanyar zamba da suka kai $190,324.
Tuhumar ta ce ya karkatar da kuɗin Henrietta Vandi tsakanin Agusta 2021 da Fabrairu 2025 a Legas.
Wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen.Lauyan masu gabatar da ƙara, Nnaemeka Omewa, ya roƙi kotu ta ba da ranar fara shari’a, ta kuma tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.
Mai Shari’a ya ɗage shari’ar zuwa 29 ga Oktoba, 2026, ya kuma umarci a tsare shi a Gidan Gyaran Hali na Ikoyi.

