Abbas Tajudeen Ya Ƙaddamar Da Takarar Wa’adi Na Biyar A Zariya

Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Abbas Tajudeen, ya ƙaddamar da takararsa ta neman wa’adi na biyar a Majalisar Wakilai ta Tarayya, yayin wani gagarumin taro da aka gudanar ranar Asabar a garin Zaria.

Taron ya samu halartar dubban magoya baya, shugabannin jam’iyyar APC, da manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, inda aka nuna cikakken goyon baya ga shugaban majalisar.

A yayin jawabin da ya gabatar, Abbas Tajudeen ya bayyana cewa ya yanke shawarar sake neman amincewar al’ummar mazabarsa ne domin ci gaba da ayyukan ci gaba da wakilcin da ya ce ya kawo tun bayan hawansa majalisar.

Ya kuma gode wa al’ummar Zariya bisa irin goyon baya da amincewar da suke ci gaba da nuna masa, yana mai alƙawarin ƙara ƙaimi wajen kawo ayyukan more rayuwa, ilimi da ci gaban matasa idan aka sake zaɓensa.

An gudanar da taron cikin ɗumbin murna da gangamin goyon baya daga magoya bayan shugaban majalisar, waɗanda suka bayyana cewa suna tare da shi domin ci gaba da wakilci a karo na biyar.

96868

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *