Kotu Ta Yanke Wa Saleh Mamman Shekaru 75 a Gidan Gyaran Hali Kan Damfarar Naira Biliyan 33.8
Kotu Ta Yanke Wa Saleh Mamman Shekaru 75 a Gidan Yari Kan Damfarar Naira Biliyan 33.8
Ta kuma umarci jami’an tsaro su kamo shiMai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba 13 ga Mayu, 2026, ya yankewa tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin shekaru 75 a gidan yari bisa laifukan almundahanar kuɗi.Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da Mamman kan zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai N33,804,830,503.73.
Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume guda 12 da EFCC ta shigar a kansa tun a makon da ya gabata, kafin daga bisani ta ɗage yanke hukunci zuwa ranar Laraba.A cikin tuhume-tuhumen, EFCC ta bayyana cewa Mamman ya haɗa baki da wasu jami’an ma’aikatarsa da wasu kamfanoni masu zaman kansu wajen karkatar da kuɗaɗen ayyukan Mambilla da Zungeru Hydroelectric Power Plant Projects ta hannun wasu kamfanoni.
An kuma tuhume shi da haɗa baki wajen biyan kuɗi har dala 665,700 ga kamfanin Mohiba Investment Ltd ba tare da amfani da cibiyar kuɗi ba, abin da ya saɓa wa dokar hana halasta kuɗaɗen haram.A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan masu gabatar da ƙara, Rotimi Oyedepo SAN, ya sanar da kotu cewa wanda aka yankewa hukunci bai halarci kotu ba, kuma lauyoyinsa ba su bayar da gamsasshen bayani kan inda yake ba.Daga nan ya roƙi kotun ta ci gaba da yanke hukunci a rashin sa tare da neman a ƙwace kadarorin da aka gano suna da alaƙa da shi.

Kadarorin sun haɗa da gidaje biyu masu ɗakuna huɗu a Ahmed Joda Crescent, Kado Estate, Abuja da kuma wani gida a Lingo Street, Wuse, Abuja.Haka kuma kotun ta amince da ƙwace kuɗaɗe daban-daban da aka samu a gidansa da suka haɗa da dala, euro, fam, rand, rupee da kudin Saudiyya.Mai shari’a Omotosho ya yankewa Mamman hukuncin shekaru bakwai-bakwai a mafi yawan tuhume-tuhumen ba tare da zabin tara ba, yayin da wasu tuhume-tuhumen suka samu hukuncin shekaru uku da biyu.Kotun ta ce hukuncin zai fara aiki daga ranar da aka kama shi, tare da umartar dukkan hukumomin tsaro na cikin gida da na ƙasa da ƙasa su kamo shi tare da miƙa shi ga hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya.Har ila yau, kotun ta umurce shi da mayar da ragowar kuɗaɗen da ba a samu dawo da su ba daga cikin N22 biliyan da aka same shi da laifin karkatarwa.
