157984

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ƙaddamar Da Kayan Yaƙi A Kebbi

Sojoji sun ƙara ƙarfafa tsaro da sabbin rundunoni da motocin yaƙi.

Rundunar Sojin Najeriya ta ƙara ƙarfafa tsaronta a Jihar Kebbi, bayan kaddamar da sabbin rundunonin soji da motocin yaƙi masu sulke 281 a wasu sassan jihar.

An kaddamar da 28 Armoured Brigade da Garrison a Birnin Kebbi, yayin da aka girke motocin yaƙin masu sulke a Yauri, sannan aka kaddamar da 381 Arms Section a Kaoje.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya jagoranci shirin, wanda Manjo Janar Bemgba Paul Koughna, Kwamandan 8 Division kuma Kwamandan Sashe na Biyu na Operation FANSAN YAMMA, ya wakilta.Koughna ya bayyana cewa sabbin rundunonin za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukan soji, inganta sa ido da kuma rage lokacin mayar da martani ga barazanar tsaro a yankin.

Ya kuma umurci Mukaddashin Kwamandan 28 Brigade, Kanal Abdullahi Umar, da ya tabbatar da samar da isasshen tallafin makamai domin gudanar da ayyukan soji yadda ya kamata.

A cewarsa, matakin zai kuma taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da sauran barazanar tsaro da ke fuskantar Jihar Kebbi da ma yankin Arewa maso Yamma.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *