154012

KOTU DAKE GARIN DAMATURU TA BADA UMARNIN TSARE LAMARBAGO

Kotu ta tsare Lamarbago kan zargin ɓata sunan kwamishinan kasafi.

Kotun Majistare ta Jiha mai lamba 1 da ke Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin tsare Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Lamarbago, a gidan gyaran hali.An tsare shi ne bisa zargin ɓata sunan Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Ci Gaban Yobe, Hon. Muhammad Garba Gagiyo.

Rahoton Daily Trust ya ce Lamarbago, wanda aka bayyana a matsayin mai sukar siyasa, yana fuskantar shari’ar ne kan zargin kalaman da suka shafi kwamishinan.

Tunda Fari Musa Abdullahi ya zargi kwamishinan da aika yaran sa su farmasa inda suka kwashe masa wayoyi da wasu abubuwa a cewarsa.

Ma dogara Daily Trust

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *