164066

Tashin hankali a Mangu: An harbi Fulani biyu, an sace shanu 70

Tashin hankali a Mangu yayin da Fulani makiyaya ke zargin jami’an tsaro da kai musu hari, bayan ‘yan bindiga sun raunata mutum biyu tare da sace shanu 70.

An samu tashin hankali a yankin Alohom-Sabon Gari da ke karamar hukumar Mangu a Jihar Filato, biyo bayan wani hari da aka ce an harbi Fulani maza biyu, tare da sace shanu fiye da 70 mallakin wani mazaunin Fulani.Sai dai bayan harbin da satar shanun, abin da ya kara jawo damuwa shi ne zargin da wasu mazauna Fulani da suka shaida lamarin ke yi cewa jami’an tsaro ne a cikin motar sulke da Hilux suka kai musu hari.

Wani shaidar gani da ido ya ce: “Da farko mun ji harbe-harbe, sai muka yi kokarin guduwa. Daga nan muka lura jami’an tsaronmu ne, sanye da bakaken kaya a cikin wata motar Hilux. Motar ta janye da sauri bayan ta harba harsashi biyu, daga baya ta dawo. Sai muka ga motocin sulke.

Wasu mutane sun ce mu gudu, amma na ce a’a, ina tsammanin sun zo ne don su kare mu. Kafin mu ankara, sun bude mana wuta, har muka tsere don tsira da rayukanmu.

“Zargin, wanda har yanzu ba a tabbatar da shi daga wani wuri mai zaman kansa ba, ya kara wani damuwa a yanayin tsaron da ke da rikitarwa a yankin, inda mazauna ke ci gaba da zargin cewa wasu jami’an tsaro na kai musu hari a cikin rikicin manoma da makiyaya.

An ce shanun da aka sace mallakin Alhaji Yako ne, wani mazaunin Fulani a yankin.A lokuta biyu, shugabannin Fulani sun nuna yatsa ga jami’an Operation Rainbow, cewa suna hadin gwiwa da kungiyoyin mayaka masu makamai wajen kai hari a al’ummomin Fulani don kora su da kuma sace musu dabbobi.

A wata tattaunawa da aka fitar, an ji wani kansila a Filato yana cewa: “Yanzu muna da jami’an tsaronmu da ke taimaka mana wajen kawar da Fulani. Don haka ba ma bukatar sojoji ma, su bar kasarmu.

“Lura: Wannan labari ne da Zagazola Makama ya bayar.

Zargin da ake yi wa jami’an tsaro bai samu tabbaci mai zaman kansa ba, kuma ba a ji ta bakin rundunar tsaro ba.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *