Ko Yana Ina Zai Gudanar Da Aikin Sa
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu ba sai yana Abuja ba kafin ya gudanar da aikinsa.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba lallai ne ya kasance a Abuja ba domin gudanar da ayyukansa na shugabancin ƙasa.
Sanarwar ta zo ne yayin da ake magana kan kasancewar Shugaban a wajen Abuja, inda Fadar Shugaban Ƙasar ta bayyana cewa shugaban ƙasa na iya gudanar da aikinsa daga sauran wuraren da yake, muddin yana ci gaba da aiwatar da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, kasancewar Tinubu a wani wuri ba yana nufin ya daina gudanar da ayyukan gwamnati ba.

