An Lalata Sansanonin Yan Ta’adda Tare Da Halaka 18
Hare-haren sama sun lalata sansanonin ’yan ta’adda, sun kashe 18 a Tumbunma BabaDaga Zagazola MakamaJiragen yaƙin saman Rundunar Sojin Najeriya ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kai hare-hare kan wasu sansanonin ’yan ta’adda da wuraren ajiyar kayayyakin yaƙi a Tumbunma Baba, cikin yankin Tumbuns, inda rahotanni suka ce an kashe kusan ’yan ta’adda 18.An gudanar da harin ne da misalin ƙarfe 6:05 na safe ranar 11 ga Satumba, 2026, bayan samun bayanan sirri cewa wasu manyan ’yan ta’adda na gudanar da wani muhimmin taro a tsibiran yankin.Majiyoyin soji sun ce bayanan leƙen asiri, sa ido da bincike ta sama (ISR) da aka gudanar ranar 9 ga Satumba sun gano wasu gine-ginen ’yan ta’adda da wuraren da suke amfani da su wajen adana kayayyakin aiki da na yaƙi.Bayan tabbatar da bayanan, jiragen yaƙin sun kai hari kan wuraren da aka gano, inda suka lalata gine-gine da dama da kuma cibiyoyin ajiyar kayayyakin da ake zargin ’yan ta’addan ke amfani da su.Hare-haren sun kuma kashe kusan ’yan ta’adda 18, wadanda ake zargin suna gudanar da ayyukansu daga wannan maboyar.Majiyoyin soji sun tantance cewa aikin ya samu nasarar kusan kashi 85 cikin 100, tare da bayar da shawarar ci gaba da kai wasu hare-haren sama domin ƙara lalata ragowar ƙungiyar da kuma hana su sake kafa sansanoni.Rundunar Sojin Najeriya ta ce irin wadannan ayyuka na daga cikin matakan da take ɗauka domin ragargaza hanyoyin sadarwa da kayayyakin tallafin ’yan ta’adda, tare da hana su gudanar da zirga-zirga da tsara hare-hare a yankin Tumbuns.

