NAPTIP Ta Yi Gargadi Kan Iyaye da Ake Zargi da Miƙa Yaransu Domin Lalata da Su a Madadin Kuɗi.
NAPTIP Ta Yi Gargadi Kan Iyaye da Ake Zargi da Miƙa Yaransu Domin Lalata da Su a Madadin Kuɗi.
Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta nuna damuwarta kan ƙaruwar rahotannin cin zarafin yara ta hanyar lalata a Najeriya, musamman waɗanda ake zargin wasu iyaye da masu kula da yara na da hannu a ciki.Daraktar hukumar, Binta Adamu Bello, ta yi gargaɗin cewa NAPTIP za ta tsaurara matakan bincike da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan laifuka domin fuskantar hukuncin da doka ta tanada.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Vincent Adekoye, ya fitar a Abuja ranar 16 ga Oktoba, 2026, daraktar ta bayyana cewa hukumar na samun rahotannin wasu iyaye da ake zargi da miƙa yaransu ga wasu mutane domin lalata da su a madadin kuɗi ko wasu alfanun duniya.
An Kama Wata Mata a AbujaDaraktar ta bayyana hakan ne bayan jami’an NAPTIP sun kama wata mata mai matsakaicin shekaru a Abuja, bisa zargin miƙa ‘yarta matashiya ga wasu maza domin su lalata da ita a madadin kuɗi.Hukumar ba ta bayyana sunan matar ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan zargin.
Binta Adamu Bello ta bayyana irin wannan hali a matsayin babban zalunci ga yara, tana mai cewa cin zarafin na iya jawo illa ga lafiyarsu, yanayin tunaninsu da makomarsu.Ta ce abin damuwa shi ne yadda wasu daga cikin mutanen da ya kamata su kare yara, kamar iyaye da masu kula da su, ake zargin su ne ke taimakawa wajen cin zarafinsu.
NAPTIP Ta Ƙara Ƙarfafa BincikeDaraktar ta ce hukumar ta ƙarfafa hanyoyin sa ido da matakan tabbatar da doka, tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaggawa da gurfanar da waɗanda ake zargi.Ta jaddada cewa hukumar ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka tabbatar da laifin cin zarafin yara ba, kuma za ta tabbatar an bi matakan shari’a da suka dace.Ta kuma bayyana cewa tun watannin baya ta bayar da umarni ga ofisoshin NAPTIP na jihohi da su ƙara sa ido, hanzarta amsa rahotannin cin zarafi da kuma tabbatar da gudanar da shari’o’in da suka shafi yara yadda ya kamata.
An Gargadi Iyaye Kan Zaɓen Ma’aikatan GidaBinta Adamu Bello ta yi kira ga iyaye da su kula da mutanen da suke ɗauka aiki ko waɗanda suke yawan zuwa gidajensu, musamman direbobi, masu kula da lambuna, ma’aikatan gida da waɗanda ke kai yara makaranta.
Ta bukaci iyaye su binciki tarihin waɗannan mutane kafin ɗaukar su aiki, tare da kula da hulɗar da suke yi da yaransu.A cewarta, wasu rahotanni da hukumar ke samu na nuna cewa ana zargin wasu mutanen da yara suka saba da su da hannu a cin zarafinsu.
NAPTIP ta kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani zargin cin zarafin yara ga hukumomin da abin ya shafa domin a gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada.
Majiyar labari: Hukumar NAPTIP, sanarwar ranar 16 ga Oktoba, 2026.

