KOTU A JIHAR GOMBE TA BADA UMARNIN SAKE ZAƁEN DAN TAKARAR PDP
Kotu ta soke tikitin Pantami na PDP a Gombe, ta umarci a sake gudanar da zaɓen fidda gwani.
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke nasarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na zaɓen gwamnan Jihar Gombe na 2027.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da wani ɗan takarar neman tikitin PDP, Usman Aliyu Garry, ya shigar yana ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami.
Kotun ta kuma umarci PDP ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani domin zaɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a Gombe, bisa tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ƙa’idojinta da dokokin zaɓe da suka dace.
Pantami ya samu tikitin PDP ne a wani zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu, inda aka bayyana cewa ya samu nasara ta hanyar amincewa da baki (voice affirmation) bayan an gabatar da shi a matsayin ɗan takara guda.
Daga baya PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta a watan Yuni. Ƙarar Garry ta ƙalubalanci sahihancin tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami, yayin da Pantami da PDP suka kare sahihancin tsarin a gaban kotu.
Hukuncin na nufin cewa PDP za ta sake gudanar da tsarin zaɓen fidda gwani a Gombe domin tantance wanda zai wakilci jam’iyyar a zaɓen gwamna na 2027.

