157383

Iran A Shirye Take Ta Sake Komawa Yaki

Araghchi: Iran a shirye take ta koma yaƙi, amma har yanzu tana buɗe ƙofar diflomasiyya.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce Iran a shirye take ta koma yaƙi idan rikicin ya sake kunno kai, har ma idan hakan ya kai ga abin da ya kira “yaƙin ranar kiyama” (doomsday war).

Sai dai ya ce Iran har yanzu tana buɗe ƙofar tattaunawa da diflomasiyya domin warware rikicin.

Kalaman Araghchi sun zo ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani shirin Iran na kwanaki bakwai da nufin kawo ƙarshen yaƙin tare da sake buɗe Mashigar Hormuz (Strait of Hormuz).

Iran ta ce tana shirye ta kare kanta idan aka ci gaba da yaƙi, yayin da kuma take nuna cewa har yanzu akwai damar amfani da hanyar diflomasiyya.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *