Gwamnatin Sokoto Ta Rufe Masallacin Lukuwa
Gwamnatin Sokoto Ta Rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa Bayan Harin KisaGwamnatin Jihar Sokoto ta ba da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke unguwar Mabera, a birnin Sokoto, har sai yadda hali ya yi, bayan tashin hankalin da ya faru a makon da ya gabata inda wani matashi ya kutsa cikin masu sallah ya caka wa malamin wuƙa.
Yadda Lamarin Ya FaruRahotanni sun ce harin ya faru ne jim kaɗan bayan idar da Sallar Juma’a, a lokacin da Sheikh Lukuwa ke gaisawa da mabiyansa kamar yadda ya saba. Matashin, wanda ke cikin masu sallah, ya kai masa hari da wuƙa, inda ya samu rauni a wuya da hannun hagu. Nan take, sauran masu masallaci suka cafke wanda ake zargi, inda suka lakaɗa masa dukan da ya yi sanadin ajalinsa, kafin jami’an tsaro su isa wurin. ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya sakamakon rikicin, yayin da aka garzaya da Sheikh Lukuwa asibiti domin kula da shi.
Dalilin Rufe MasallacinCikin wata sanarwa da Darakta-Janar kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a a Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai tare da kisan da ya biyo baya. An ayyana masallacin a matsayin wurin aikata babban laifi, har sai an fitar da sabon umarni.Gwamnati ta kuma kafa kwamitin malamai domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin, inda ake sa ran kwamitin zai ba wa gwamnati shawarwari kan matakan da suka dace a ɗauka domin kare martaba da maslahar jihar.
Rikicin Ya Samo Asali Ne Daga Ina?Wasu rahotanni sun danganta harin da wasu tsoffin kalamai da Sheikh Lukuwa ya taɓa yi a wani wa’azinsa, waɗanda suka jawo ce-ce-ku-ce da barazana a baya. An ruwaito cewa malamin da wasu mabiyansa sun taɓa kai ƙorafi ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar kan barazanar da suke fuskanta daga wani matashi mai suna “Mai Barewa,” wanda aka taɓa kamawa bisa zargin yunƙurin cutar da malamin, kafin kotu ta ƙi ba shi belin, lamarin da ya taɓa jawo zanga-zangar wasu matasa a manyan tituna a birnin.
Matsayin GwamnatiGwamnatin Sokoto ta nesanta kanta daga duk wani mai fakewa da addini don yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), iyayensa, iyalansa, ko Sahabbansa. Ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalamai masu tayar da hankali ko rura wutar rikici, waɗanda za su iya tunzura jama’a da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan da aka daɗe da santa jihar Sokoto da shi.A nata ɓangaren, Rundunar ‘Yan Sanda ta kuma fitar da gargaɗi kan yiwuwar ƙarin hare-hare a makarantu da wuraren ibada, inda ta umarci kwamishinonin ‘yan sanda da sauran sassan tsaro da su ƙara sa ido da sintiri a jihar.Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne mai bin fahimtar Ahlussunnah Wal Jama’a a Sokoto, kuma yana daga cikin malaman da suka shahara wajen janyo taƙaddama, musamman dangane da al’amura masu sarƙaƙiya.
