153371

Gwamnoni Shida Ne Kacal Na Arewa Suka Goyi Bayan Tunubu

Shettima: Gwamnoni 6 kacal daga cikin 19 na Arewa ne suka goyi bayan Tinubu a 2023Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa daga cikin gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya, guda shida kacal ne suka goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, sarautar Sardaunan Ilorin.Ya ce duk da hamayyar siyasa da matsalolin da suka dabaibaye takarar Tinubu a lokacin, Tinubu bai karaya ba, kuma ya ci gaba da neman kujerar shugaban ƙasa.Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce bayan zaɓen 2023, Tinubu ya sasanta da wasu daga cikin gwamnonin Arewa waɗanda ba su goyi bayan takararsa ba. Ya yi amfani da hakan wajen kira ga ’yan siyasa da su guji mayar da bambancin ra’ayin siyasa zuwa gaba ta dindindin.Shettima ya kuma yi kira ga ’yan siyasar Kwara da su zauna lafiya bayan zaɓen fidda gwani na APC, ba tare da la’akari da wanda ya samu nasara ba.A yayin ziyararsa ta Kwara, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙaddamar da Kwara State Revenue House da kuma wata masana’antar ɗinki a Ilorin.

Madogara: Daily Trust / Daily Post

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *