IGP Ya Ziyarci EIB Don Karfafa Tsaro

IGP Disu Ya Ziyarci Rukunin Kamfanonin EIB Domin Ƙarfafa Fasahar Tsaro Da Ayyukan ‘Yan Sanda.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu ya kai ziyarar aiki zuwa rukunin kamfanonin EIB ƙarƙashin jagorancin shugabansa, Dakta Bright Echefu domin ƙarfafa fasaha da inganta ayyukan rundunar ‘yan sanda.

A yayin ziyarar IGP Disu ya zagaya wasu muhimman cibiyoyi da suka haɗa da EIB Stratoc Limited da ke Idu, wadda ke samar da hanyoyin sa ido na zamani Poctova mai ƙera kayan jami’an tsaro.

Shugabannin rundunar sun bayyana cewa haɗin gwiwar na da nufin ƙarfafa ikon rundunar wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro ta hanyar amfani da sababbin fasahohi da dabarun zamani.

Briech UAS da ke Kuje mai kera jiragen sama marasa matuƙa (drone), da kuma Giga Forensics da ke Idu, mai samar da hanyoyin binciken ƙwaƙƙwaran hujjoji da fasahar sa ido.

Ziyarar ta nuna ƙudirin rundunar ‘yan sandan Najeriya na rungumar fasahar zamani tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin inganta tattara bayanan sirri, binciken manyan laifuka, da haɓaka ingancin ayyukan tsaro.

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *